fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Kwana daya bayan kashe mutane sama da 35, ‘yan Bindiga sun sake shiga kauyukan Zamfara sun kashe mutane 6

Lamarin ya farune a kauyen Gora Namaye dake karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

 

Wata Majiya ta gayawa Channels TV cewa maharan sun shiga garin da misalin karfe 3 zuwa 4 na yammacin jiya, Laraba inda suka kashe mutane 6 da jikkata wasu da dama.

 

Kokarin jin ta bakin ‘yansanda akan lamarin ya faskara. Kwana daya kenan da ‘yan Bindigar suka kashe mutane sama da 35 a kauyukan Maradun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *