fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Kwanan mu 56 ba mu yi wanka ba>>Daliban makarantar da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Daliban makarantar Kwalejin Forestry dake Afaka Kaduna da suke bayyana yanda suka kasance a hannun wanda suka yi garkuwa dasu sunec sun sha wahala sosai.

 

Daya daga cikin abinda suka rika kuka dashi shine kwanansu 56 basu yi wanka ba.

 

An dai sako daliban daga baya inda Sheikh Ahmad Gumi da Tsohon Shugaban kasa,  Olusegun Obasanjo suka shiga tsakani.

 

Saidai har yanzu babu duriyar yanda ta kasa ce da sauran daliban jami’ar Greenfield dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da aka sace.

 

Amma Sheikh Gumi ya bayar da tabbacin cewa, suma ana kan tattaunawa dasu, inda yace sun fasa Aniyarsu ta kashe daliban.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *