fbpx
Monday, September 27
Shadow

Kwanannan mulkin Najeriya zai gagari Shuwagabanni>>Obadiah Mailafia

Tsohon Mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya yace kwanannan mulkin kasar zai gagari Shuwagabanni.

 

Ya kuma bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari na da shirin mayar da Najeriya kasar Musulmai da ta Fulani.

 

Yace idan ba’a dauki mataki akan lamarin talauci ba to lallai akwai matsala da ba za’a iya maganinta ba.

 

Yace akwai Mutane Miliyan 90 dake fama da talauci a Najeriya kuma kaso 50 a Arewa suke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *