fbpx
Monday, September 27
Shadow

Kwankwaso ya bayyana abinda ya faru bayan haduwarsa da Gwamna Ganduje

A karon farko, tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana yadda haɗuwarsa ta kasance da abokin takun saƙarsa na siyasa, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a filin jirgin saman Abuja, babban birnin Najeriya.

Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC Hausa cewa ya riga Gwamna Ganduje zuwa filin jirgin da kamar awa guda, a lokacin ne ya samu labarin cewa shi ma magajin nasa na kan hanyar isowa filin jirgin.

“Na ce to Allah ya kawo shi, kasuwa ce ai kamar tasha ce, ba wanda za ka ce ya zo ko kar ya zo, muka shiga jirgi daya da shi muka taho, muka sauka a wanan tasha ta Kano, na kama hanyata ya kama tasa ya tafi gida.”

Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ”A matsayi irin na Musulunci ai ba lallai sai kana jam’iyya daya da mutum za ka gaisa da shi ba, mun gaisa da shi kowa ya koma ya zauna a kujerarsa, don haka haka muka isa har Kano kowa na zaune a kujerarsa.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *