fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Lauya ya kai kara kotu inda ya nemi a hana majalisa tantance sabon shugaban EFCC

Wani Lauya, Osuagwu Ugochwukwu ya kai kara babbar kotun Gwamnatin tarayya dake Abuja inda yake neman ta hana rantsar da sabon shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa.

 

Shugaba Buhari ya aikewa da majalisa sunan Bawa inda yake neman su amince dashi a matsayin sabon shugaban EFCC. Dan shekaru 40 ya shafe shekaru 15 yana aiki da hukumar inda a yanzu yake a mataki na 13.

 

Dokar EFCC ta nemi sai wanda ya kai matsayin darakta da kuma Akawu a maaikatar kamin ya zama shugaban hukumar. Ko kuma wanda ya kai matsayin mataimakin kwamishinan ‘yansanda ko kuma kwatankwacin haka.

 

Ana tsammanin Abdulrashid Bawa na da kusanci da Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami wanda ya taka rawa wajan sauke Ibrahim Magu. Dukan sudai daga jihar Kebbi suka fito.

 

Lauyan ya bayyana cewa yana neman kotu ta fayyace shin Bawa ya cancanci zama shugaban EFCC saboda mukamin da yake dashi a hanzu bai kai daidai da mataimakin kwamishinan ‘yansanda ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *