fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

Lauya ya maka diyar shugaban kasa, Hanan Buhari a kotu saboda amfani da jirgin shugaban kasar zuwa Bauchi

Wani lauya a babban birnin tarayya, Abuja, Oluwatosin Ajaomo ya maka diyar shugaban kasa, A’isha, wadda aka fi sani da Hanan Buhari a kotu game da amfani da jirgin shugaban kasa da ta yi zuwa Jihar Bauchi a ranar 10 ga watan Janairu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Lauyan a takardar karar daya gabatar ya bukaci kotu data tirsasawa Hanan Buhari mayar da kudin man da aka zubawa jirgin ta yi wannan tafiyar dadhi sannan kuma ta mayar da kudin da aka kashe wajan amfani da jirgin a wannan tafiya tata.

Ya kuma bukaci kotu data hana Hanan Buhari kara amfani da jirgin a nan gaba matukar ba ta zama ma’aikaciyar gwamnati ba.

Lauyan ya bayyanawa Punch cewa zai gabatarwa da da hanan Buhari da sammacin Kotun da kanshi wanda idan hakan bai samu ba zai bukaci kotun ta bashi damar mikawa Hanan Sammacin ta wata hanya daban.

Tun dai a wancan lokacin Me magana da yawun shugaban kasar ya kare Hanan Buhari kan amfani da jirgin saman inda ya bayyana cewa ta bi ka’ida wajan amfanin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *