fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Likitoci sun fara yajin aiki duk da sanya hannu kan yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Likitocin Kasa (NARD) a ranar Alhamis 1 ga watan Afrilu sun fara yajin aiki na ba-sani-ba-sabo duk da gudanar da wani taro tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya a ranar Laraba 31 ga Maris.

An bayyana cewa an sanya hannu kan wata yarjejeniya bayan ganawar tsawon awanni 7 tsakanin Gwamnati da shugabannin NARD a ofishin Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige.

Batutuwan da likitocin da suka fada a cikin Takaddamarsu ta sun hada da rashin biyan albashin wasu ma’aikatan gida, rashin daukar ma’aikatan gida, soke kudin benci ga likitocin da ke karbar horo a wasu asibitocin, rashin biyan mafi karancin kudin na Kasa tare da tattauna kan batun alawus.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Ngige ya bayyana cewa duk abubuwan da aka rubuta a cikin MOA za a aiwatar da su.

Ya kuma ce an sanya musu lokaci, kuma za su sake haduwa don duba ayyukan da aka bayar, don sanin wanda ya yi da wanda bai yi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *