fbpx
Saturday, July 24
Shadow

Lionel Messi ya zamo biloniya na biyu a tarihin wasan kwallon kafa

Bayan Cristiano Ronaldo ya zamo biloniya na farko a harkar wasan kwallon kafa, abokin takarar shi Lionel Messi shima yanzu ya zamo biloniya na biyu a tarihin wasan kwallon kafa a cewar mujallar Forbes.

Mujallar ta kara da cewa Messi yafi gabadaya yan wasan kwallo kafa daukar albahi mai tsoka a 2020, bayan da dan wasan Argentinan zai dauki albashin yuro miliyan 98 wanda suka hada da albashin shi na yuro miliyan 72 sai kuma karin yuro miliyan 26 na tallace tallace.
Kamfanonin da Messi yake yiwa talla sun hada da Adidas,Pepsi,Budweiser Al-Vision da kuma Ocam Technologies. Cristiano Ronaldo shine yazo na biyu a wannan shekarar bayan messi yayin da tauraron Juventus din zai dauki albashin yuro miliyan 91 a 2020 sai kuma Neymar na uku da albashin yuro miliyan 75.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *