fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Liverpool zata sake sayo tsohon dan wasanta,Coutinho

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool na kokarin dawo da tsohon dan wasanta data sayarwa da Barcelona, dan kasar Brazil,  Philippe Coutinho.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A shekarar 2018 ne liverpool ta sayarwa da Barca Coutinho akan Fan Miliyan 142 saidai tun bayan barin Liverpool dan wasan ya kasa tabuka abin a zo a gani inda a yanzu haka Barca ta baiwa Bayern Munich aronshi.

Kocin Liverpool,Jurgen Klopp na neman dan wasan tsakiya kuma yana hangen sayen dan wasan Bayer Leverkusen, Kai Havertz.

Idan an bude kasuwar saye da sayarwar ‘yan wasa Liverpool ke son sayen dan wasan wanda idan bata yi nasarar sayenshi bane zata koma kan tsohon dan wasan nata, Coutinho, kamar yanda Express Sports ta ruwaito.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *