fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Ma’aikata sun yi karanci a Amurka, Masu gidajen Abinci da na neman ma’aikata Ruwa a Jallo

A yayin da annobar cutar coronavirus ta mamaye kusan duka Duniya kuma ta taba bangarorin rayuwa da dama, a kasar Amurka kuwa, Masu gidajen Abinci ne ke neman ma’aikata amma mutane basu son yin aikin.

 

Boredpanda ta ruwaito cewa, wasu gidajen Abincin na neman Ma’aikata Ido rufe. Saidai babu masu neman aikin. Rahoton yace mutane na korafin cewa, ba’a girmamasu a gidajen abincin da suke aiki.

 

Ya kara da cewa, ba wai maganar rashin girmamawar bane kawai, hadda rashin biyan Albashin da ya kamata.

 

Mutane dai sun hau shafukan sada zumunta inda suke korafi akan lamarin. Wani ya bayyana cewa yasan masu gidajen Abinci da yawa da suke ta faman neman ma’aikata amma babu. Rahoton yace,yawancin ma’aikatan bangaren gidajen abincin ko dai sun ajiye aikin sun koma gwamnati na biyansu kidin rashin aiki ko kuma sun canja sana’a gaba daya.

 

Ga abinda wasu suke cewa kan lamarin:

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *