fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ma’aikatan Kiwan lafiya Sun Fara Yajin Aiki a Jihar Nasarawa

Ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Nasarawa sun fara yajin aikin sai baba ta gani don biyan bukatunsu na inganta walwala.

Mai magana da yawun ma’aikatan, Mista Kyari Caleb, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa mambobin kungiyar sun amince da matakin da aka yanke a taron da kungiyar ta gudanar.

A cewarsa, wasu daga cikin korafin nasu sun hada da rashin samun karin girma a tsakanin mambobin tun daga shekarar 2011, rashin aiwatar da N30,000 mafi karancin albashi ga mambobinta da kuma rashin karin albashi da sauransu.

Ya kara da cewa gamayyar sun yi haƙuri, yana cewa ‘’ amma an tura mu bango. ’’

Ya ci gaba da cewa a watan Yunin 2020 kungiyar ta fara yajin aiki a kan batutuwa guda daya, amma sai ta dakatar da yajin aikin bayan gwamnatin jihar ta yi kira gare ta.

Shugaban ya jaddada cewa bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU), gwamnatin ta yi alkawarin fara aiwatar da bukatunsu ba tare da bata lokaci ba, ya kara da cewa gwamnatin ta saba alkawarin da ta yi tun shekarar 2020.

Ya ce mambobin kungiyar a dukkanin manyan kiwon lafiya na jihar sun janye ayyukansu daga ranar Litinin, 7 ga Yuni, 2021, har zuwa wani lokaci.

Ya tabbatar da cewa mambobin za su ci gaba da zama a gida har sai gwamnati ta yi abin da ake bukata.

Dangane da shirin yajin aikin da aka shirya, Shugaban Ma’aikata na Jihar Nasarawa, Mista Nicholas Aboki, tun farko a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a, 4 ga Yuni, 2021, ya bukaci kungiyoyin da su dakatar da shirin yajin aikin da suke shirin yi, yana mai cewa gwamnati na aiki tukuru don inganta walwalarsu.

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta fara biyan sabon N30,000 na mafi karancin albashi na kasa, amma ga ma’aikatan gwamnati daga matakin aji 1-6 ne kawai za su amfana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *