fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Ma’aikatun mu sun cika dan haka zaka iya kammala karatu da Digiri me kyau daga makaranta me kyau amma ka rasa aiki>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jaddada maganarsa ta cewa matasa idan suna son samun aiki to su nutsu su daina tada fitina dan masu zuba Jari su ga damar zuwa Najeriya.

 

Ya bayyana hakane a hirar da ake yi dashi yanzu haka a gidan talabijin na kasa, NTA, wadda wakilin hutudole.com yake bibiya. Yace bayan Zanga-Zangar SARS,  ya tura ministocin sa mazabunsu dan su tattauna da jama’a.

 

Yace ya gaya musu su tattauna da shuwagabannin jama’a, sarakuna da sauransu. Shugaban yace musamman matasa, ya ce a gaya musu ma’aikatun gwamnati sun cika, dan haka mutum zai iya kammala karatu da Digiri me kyau, daga makaranta me kyau amma ya rasa aikin yi.

 

Yace dan haka matasan sune zasu wa kansu abu me kyau, idan suka zauna Lafiya ta yanda kamfanonin kasashen waje zasu zo su zuba jari dan su samu aikin yi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *