fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Mabiya addinin kirista sun lakadawa wani fasto duka a coci bayan da yace su tara masa kudi

Fasto James Mugo ya sha dukan kawo wuka a hannun mutanen cocinsa wanda har ta kai ga an kaishi Asibiti.

 

Lamarin ya farune yayin da ake taron sabuwar shekara a cocinsa kuma ya nemi mutanen cocin su tara masa kudi amma suka kiya.

 

Abin ya farune a kasar Kenya inda faston yace duk wanda bai biya kudin ba zai masa addu’a ba zai zamu albarka ba a shekarar 2022.

 

Ya nemi kowanne ya bayar da kudin Kenya, Ksh. 4,200 wanda yayi daidai da kwatankwacin Naira dubu 16,000 amma sai rigima ta kaure aka hanashi.

 

A karshe dai an masa duka wanda har sai da ya kwanta a Asibiti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *