fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mafarauta da ‘yan banga sun ceto wasu mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kogi

Kungiyar mafarauta ta Najeriya, tare da rundunar ‘yan banga ta jihar Kogi, a ranar Litinin, sun kai samame a kogon masu garkuwa da mutane inda aka cafke uku daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanen sannan aka kubutar da Fulani uku.

Bayanan da aka samu sun bayyana cewa an yi garkuwa da wasu Fulani daga yankin Chikara a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja kwanaki 13 da suka gabata ta hannun wani gungun masu garkuwa da mutane.

Kakakin kungiyar mafarautan, Abdullahi Yahaya, ya bayyana cewa yaran da sukayi aikin ceton basu ji rauni ba kuma suna cikin koshin lafiya yayin da aka mika masu garkuwa da mutanen ga hukumomin da suka dace, tare da kwace makamai don ci gaba da bincike.

Yahaya ya yabawa gwamnatin jihar da kwamishinan ma’adanai, Engr Bashir Gegu, saboda tallafin da suke bayarwa wajen samar da kayan aiki don ayyukan su a yankin.

Da yake mayar da martani game da ci gaban, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na jihar Kogi, Commodore Jerry Omodara (mai ritaya), ya ce irin wannan nasarar da jami’an suka samu ta tabbatar da tsaro na tabbatar da cewa cibiyar tsaro ta jihar tana da ƙarfi don magance duk wasu munanan laifuka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *