fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Maganar ci gaba da zaman Shugaban kasa a Arewa ba abune da zai yiyu ba>>Afenifere

Kungiyar kare muradun yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa, ba zasu yadda da maganar ci gaba da zaman shugabancin Najeriya a Arewa ba nan da shekaru 4 masu zuwa.

 

Kakakin Afenifere Jare Ajayi ne ya bayyana haka inda yace sam hakan ba abune da zai yiyuba.

 

A baya dai, Shugaban Kungiyar Matasan Arewa, Yerima Shattima yayi maganar cewa, Arewa zata ci gaba da mulki nan da ashekaru 4 bayan Shugaba Buhari ya kammala mulki kamin ta mikawa kudu.

 

Yerima yace indai maganar karba-karba za’a yi to ai Goodluck Jonathan mulkin ‘Yaradua ne ya vika ba nashi ba. Dan haka sai an ramawa Arewa, akan wannan ne dai Afenifere tace bata yadda ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *