fbpx
Monday, October 25
Shadow

Magidanci ya dirkawa matar makwabcinsa ciki har ta haihu, yace Makwabcin nasa raggo ne

Mijin matar ya nemi diyyar Dala Miliyan $4.5 daga wajan makwabcin nasa.

 

Mijin, Murambiwa Murangariri ya kai kara kotu inda ya nemi a tursasawa makwabcinsa, Tineyi Lavite Tapfumaneyi, biyan diyyar.

 

Yace abinda makwabcin nasa yayi ya kawo rudani a gidansa.

 

Murambiwa yace makwabcin nasa ya taba yin lalata da matarsa a baya inda har yake gaya masa bakar magana ta cewa wai shi ba cikakken Namiji bane.

 

Yace ya kaishi kotun gargajiya inda aka cishi tara ashe bai dena bin matar tasa ba. Yace shi da matarsa da suke da yara 4 aurensu ba zai taba dawowa daidai ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *