fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Magidanci ya kona hannun dansa saboda ya saci kifin miya

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kame wani magidanci da ya kona hannun dansa a wuta bisa zarginsa da satar kifin miya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa magidancin mai suna Idowu Sikiru, ya kusan halaka dansa Segun mai shekaru biyar inda ya yi masa dukan kawo wuka ya kuma sanya hannun yaron a kaskon tuya da ya dora sa akan wuta ya kuma kona bakin yaron ba ya zaunar da shi a kan kaskon tuyan ya soye masa mazaunansa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ya ce, an garzaya da yaron asibiti inda ake kokarin ceton rayuwarsa yayin da rundunar ke ci gaba da bincikar wanda ake zargin kafin daga bisani a gurfanar da shi a kotu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *