fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Magidanci ya lakadawa matarsa duka har ta mutu saboda ta ki yadda su yi kwanciyar aure

Wani mutum ya lakadawa matarsa duka har ta mutu saboda ta ki yadda su yi kwanciyar aure.

 

Matar me suna Ugieki Asemota, ta dawo daga wajan Biki inda ta iske mijinta yayi tatul da giya. Sai ta yi wanka ta shiga daki ta kulle da gudun duka, kamar yanda ya saba mata duk in ya sha giya.

 

Saidai can tsakar dare, mijin ya zo yana kwankwasa mata kofa inda ya nemi su yi kwanciyar aure amma ta ki bude masa kofar.

 

Ko da ta ga yana niyyar balle kofar, sai ta dira ta taga ta tsere amma ya bita da gudu ya kwada mata katako, ta fara zubar da jini, aka garzaya da ita Asibiti, amma kuma acan ta Mutu.

 

Lamarin ya faru a ranar 27 ga watan Yuni, kuma tuni an kama Mijin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *