fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Magidanci ya lalata rayuwar wata budurwashi da sunan zai aureta(zina har a cikin watan Azumi)

Wannan labarin wata yarinyace “yar shekaru ashirin da haihuwa, me ban takaici da ban haushi, ta wani fannin yana da ban tausayi, yarinyar ta aikawa me shafinnan na jarumane labarin abinda ya faru da ita, gadai takai taccen abinda labarin ya kunsa.
Yarin yar tace ta gamu da wani mutumne(magidanci), yace yana sonta, a karin farko bata kulashiba, amma irin yanda yaketa mata maganar aure, sai hankalinta ya fara karkata kanshi har suka fara shakuwa, wata rana suna tare sai yaga wani hotonta a cikin wayarta, tana ninkaya a ruwa, sai yacemata aikuwa zaiso yaganta a zahiri tana ninkaya, ya mata tayin suje Mijibir Park, tacemai a’a, yayita rokonta, ta nuna bata yarda dashiba, kar yaje yayi lalata da ita, yayita mata rantsuwa da Allah babu abinda zai faru, har yake cemata, shimafa yana da ‘ya ‘ya mata, saboda haka yasan muhimmancin tsare martabarsu.
A karshe ta yarda, suka tafi, suna zuwa kuwa sai ya kama daki, tayi turus, ta tambayeshi me zakayi da daki kuma?, sai yacemata ai ke na kamawa, saboda idan zaki canja kaya, ko kinasoki canja gaban mutane?.

Sai ta yarda, ta shiga daki dan canja kaya, tana ciki sai gashi ya shigo, ya matsa kusa da ita, tacemai bakace bazaka nemeniba? nan dai ya kalamlamceta ya kuma gayamata ai taba jikinta kawai zaiyi, bazaiyi lalata da itaba, daga nan dai har saida ya biya bukatarshi da ita, duk da tana cemai a’a bataso, amma yafi karfinta(kamar yanda tace, bata taba yiba, takanyi rungume-rungume da samarinta amma shine na farko daya santa a ‘ya mace).
Nan ta rasa inda zata saka kanta, itadai bata isa tace yayimata fyadeba, saboda ita ta biyoshi, gasu har a cikin daki, nan tacemai su rabu, amma yaki yarda yacemata duk da yana da aure amma bai taba jin wadda ta gamsar dashi ba irinta, saboda haka tabbas zai aureta, maganar rabuwa tsakaninsu babu ita.
Hakanan ta hakura da kalamanshi na yaudara, sukaci gaba da soyayya, kuma yarika lalata da ita duk lokacin da yakeso, har cikin azumi, a gidan mahaifinta kai koda tana jini idan yanaso yayi lalata da ita sai yayi.
Maganar aure kuwa sai yayita jan zance, da abu ya kusa kamar za’ayi sai ya bijiro da wata matsala yanda maganar zata wargaje, gashi gidansu sun fara matsamata da cewa yaushe zai fito suyi aure?, ita kuma ba abin ta gayawa mahaifiyartaba, kamar yanda tace zata iya samun ciwon da zaiyi sanadin ajalinta dalilin wannan labarin. Har rashin lafiya tayi aka kaita asibiti, likita yace hawanjini ke damunta, mahaifinta yayita mata fada akan tunanin me takeyi haka, me ta nema ta rasa da zata sawa kanta tunani?, yarinyar tace tana da samari masu nuna cewa da gaske aurenta zasuyi,amma bataso ta basu fuska tunda wannan yayi lalata da ita shine ya kamata ya aureta amma gashi yaki yayi magana.
Yanzu dai abinda yarinyar take nema shine a taimaka mata shi wannan saurayin nata ya aureta, tunda yayi lalata da ita, to amma babu wata hanyar sadarwa data bayyana da za’a sameta haka kuma tayi rokon da’a sakaya hotonta saboda kada wadanda suka santa su ganeta, yanzu saidai shawara da addu’a kawai al’umma zasu tayata dashi da kuma iyayae masu ‘ya ‘ya mata su dauki darasi akan wannan labarin su kara sa idanu akansu, dasu kansu ‘yan matan, da yayye maza kuma kuna da gudumuwar da zaku bayar.
Idan kanaso ka karanta labarin cikin hotuna dalla-dalla yanda ya faru to gashinan a kasa(amma akwai kalaman batsa da akayi amfani dasu wajan bayar da labarin)

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *