fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mahaifi ya kashe dansa me shekaru 2 ya tsere

Wani mahaifi ya daki dansa me shekaru 2 da haihuwa har ya mutu inda kuma ya tsere ya bar garinsu.

 

Mahaifin wanda dan asalin jihar Delta ne, yana zaune a jihar Bayelsa.

 

Mahaifiyar yaron bata tare da mahaifin.  Kuma makwabta sun bayar da shedar cewa yakan yiwa yaron dukan da ya wuce misali.

 

Saidai ranar da abin ya faru bayan ya gama yiwa yaron duka, ya garzaya ya kaishi Asibiti inda daga can ya tsere.

 

Wata kungiyar lauyoyi mata ta sha Alwashin bin kadin lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *