fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Mahaifi ya yanke nonon diyarsa saboda suna girma da yawa

Wani mahaifi a jihar Legas, Adegboyega ya yanke nonon diyarsa me shekaru 8 saboda yana girma da yawa.

 

‘Yansanda sun tabbatar da kama mutumin.

 

Nonon yarinyar na bangaren hagu gaba daya babu shi an yanke bayan da mahaifin yayi amfani da karfe me zafi dan hanashi fitowa.

 

Da aka matsi mahaifin, ya dorawa matarsa laifin abinda ya faru.

 

Zadai a gurfanar dashi a kotu nan da ranar Litinin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *