fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mahaifin kakakin majalissan jihar Zamfara ya mutu a hannun yan bindiga da suka sace shi

Alhaji Abubakar, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Nasiru Magarya ya mutu yayin da ake garkuwa da shi a gurin yan bindiga.

Mahaifin Kakakin wanda shine Hakimin kauyen Magarya yan bindiga sun yi garkuwa da shi makonni takwas da suka gabata tare da matarsa, jariri dan makonni uku da wasu mutane uku.

Yayin da aka ceto wadanda aka sace jiya, mahaifin kakakin baya cikin su.

Da yake magana da manema labarai, babban yayan mamacin, Malam Dahiru Magarya wanda yana cikin wadanda aka sace ya ce, mahaifin kakakin ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

“Daya daga cikin shugaban yan bindigar da aka fi sani da Kachalla ya sanar da ni cewa dan uwana ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin da yake tsare. Mun rabu lokacin da suka yi garkuwa da mu, sun kai dan uwana zuwa wani sansanin Kachalla, daya daga cikin kwamandojin ‘yan fashin ne ya ba ni labarin rasuwar dan uwana wanda ya faru sakamakon bugun zuciya sa’o’i kadan kafin ceton mu, ” yace.

Daya daga cikin matan marigayin mai suna Hauwa’u Magarya da aka yi garkuwa da ita tare da jaririnta na wata uku ta ce ta kuma samu labarin mutuwar mijinta daga hannun ‘yan bindigar.

Gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su yi magana kan batun ba.

Kokarin zantawa da kakakin majalisar ya ci tura saboda an kasa samun lambobin wayarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *