fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mahara sun kashe mutane 12 a Jihar Flato

Rahotanni daga jihar Flato na cewa wasu mahara da aje zargin makiyayane sun kashe mutane 12 a kauyen Kulben dake karamar hukumar Mangu Jihar Flato a yau, Alhamis.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Terna Tyopev, me magana da yawun hukumar ‘yansandan jihar ya tabbatar da wannan harin da aka kai da sanyin safiyar yau. Ya kara da cewa an aika da jami’an ‘yansanda dan hana sake faruwar hakan saidai yace babu wanda aka kama akan wannan lamari.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin inda yake tattaunawa da gwamnan jihar ta Flato, Simon Lalong da jami’an tsaro dan jin ba’asin abinda ya faru da matakin da za’a dauka kan lamarin.

Gwamna Lalong na Flato na daya daga cikin gwamnonin Arewa da suka goyi bayan janye Sojoji daga jiharsu inda ya bayyana cewa matakin janye sojojin na gwamnatin tarayya yayi daidai ganin cewa zaman lafiya ya fara dawowa a jihar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *