fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Maharin da ya kai bam cocin Kaduna mahaukaci ne>>Inji mahaifinsa

Mahaifin Nathaniel Samuel, matashin da aka cafke yana yunkurin tayar da bam a harabar Majami’ar Living Faith da ke jihar Kaduna ta Najeriya ya ce, dansa na fama da tabin hankali, inda har ta kai ga kwantar da shi a asibitin mahaukata a shekarar 2012 a cewarsa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kazalika Mr. Samuel Ezekiel ya tabbatar cewa, dan nasa mabiyin addinin Kirista ne kuma ba Musulmi ba ne kamar yadda wasu ke ta yadawa a shafukan sada zumunta.

Kodayake manema labarai a Najeriya da suka hada da jaridar Daily Trust sun ce, sun tuntubi mahukuntan asibtin mahaukatan na Federal Neuro Psychiatric Hospital na Kaduna da aka ce an kwantar da Samuel a shekarar 2012, amma jami’an asibitin ba su gasgata ko kuma karyata zancen kwantar da shi ba.

Darektan asibitin, Farfesa AbdulKareem Jika Yusuf ya bayyana cewa, Hukumar asibitin ba za ta iya sakin bayanan marasa lafiyarta ba ga duniya.

A cewar mahaifin nasa, dansa Samuel ya kwashe shekaru yana kwankwadon kwayoyi, yayin da danginsa suka kwantar da shi a asibitin na mahaukata a ranar 6 ga watan Disamban 2012.

Mahaifin ya ce, ya kadu matuka da labarin yunkurin dansa na tayar da bama-bamai a Cocin, yayin da ya bayyana fargabarsa kan adadin rayukan da za su salwanta da ya yi nasarar tayar da bam din.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *