fbpx
Friday, January 21
Shadow

Mai faɗar “Dan Kashiful Gummati” a wajen tafsirin Isa Waziri a Kano ya rasu

Alhaji Kabiru Usman Sanka ya rasu a yau talata.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Usman ya rasu bayan wata rashin lafiya da har yanzu ba a kai ga baiyana ta ba.

Kafin rasuwarsa, muryar marigayin sananna ce a gidajen rediyon Kano ga ma’abota jin fitaccen karatun tafsirin alƙur’ani mai girma na Marigayi Sheikh Isa Waziri.

Muryar marigayin ta yi suna, musamman a shekaru sama da ashirin da su ka gabata sakamakon yadda ya ke yawan faɗin “Allah Ya saka da alkhairi, dan Kashiful Gummati”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *