fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Maimakon tallafin man fetur, Gwamnatin tarayya zata rabawa ‘yan Najeriya Naira Dubu biyar-biyar

Gwamnatin tarayya zata rabawa ‘yan Najeriya Miliyan 40 tallafin Naira Dubu 5 kowannensu a maimakon tallafin man fetur.

 

Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka, tace wanda suka fi fama da talauci ne za’a baiwa kudin a Najeriya.

 

Tace ba zasu iya ci gaba da bayar da tallafin man fetur din ba saboda yana illa ga tattalin arzikin Najeriya.

 

Tace a tsakiyar shekarar 2022 ne za’a cire tallafin gaba daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *