fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Majalisa na son a kama Gwamnan CBN, Shugaban NNPC da sauransu, ji laifin da suka yi

Kwamitin majalisar wakilai dake saka ido kan yanda ake kashe kudin Gwamnati ya bayyana cewa, yana son a kamo wanda suka ki zuwa gabansa su yi bayanin yanda suka kashe kudin ma’aikatunsu.

 

Kwamitin yace duk wanda basu aika da wani dalili na rashin zuwa su yi bayanin ba suna son a kamosu.

 

Hakan na kunshene cikin Rahoton da kwamitin ya aikewa da majalisar na kammala bincikensa.

 

Daga cikin wanda basu bayyana a gaban majalisar ba akwai Gwamnan babban bankin Najeriya,  Godwin Emefiele da Shugaba  NNPC, Mele Kolo Kyari, da me kula da ma’aikatar Naina Delta, Effiong Akwa da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *