fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Majalisar Dattijai ta baiwa iyalan wanda Hadarin jirgin ruwa ya rutsa dasu a Kebbi Miliyan 10

Majalisar Dattijai ta baiwa iyalan wanda hadarin jirgin ruwa ya rutsa dasu a jihar Kebbi miliyan 10.

 

Mutane sama da 80 ne Rahotanni suka bayyana cewa sun mutu a hadarin jirgin ruwan da ya fatu a karamar hukumar Ngaski dake jihar.

 

Sanata Adamu Aleiro ne ya bayyana wannan kyautar kudi yayin ziyarar jaje da ya jagoranci wakilan majalisar suka kaiwa al’ummar jihar, yace za’a baiwa Sarkin Yawuri kudin dan rabawa iyalan mamatan.

 

Yace kuma hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa zata yi bincike dan cire abubuwan dake yawan kawo hadarin jirgin ruwan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *