fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Majalisar Dattijai ta bukaci hukumar soji ta kafa Rundunar musamman a Auno, Jihar Borno

A zamanta na yau,Majalisar dattijai ta yi Allah wadau da harin da Boko Haram ta kai Garin Auno na Maiduguri wanda rahotanni suka bayyana cewa ya kashe mutane 30.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Majalisar ta kuma bukaci hukumar Soji data gaggauta kafa sansanin jami’an tsaro a garin dan kare sake aukuwar lamarin nan gaba. Ta kuma bukaci hukumar kula da ibtila’i data gaggauta fara kai kayan agaji yankin.

Tsohon gwamnan jihar ta Borno, Sanata Kashim Shattima dake wakiltar mazabar Borno ta tsakiyane ya taso da batun a zauren majalisar.

Matafiya dake kan hanyar shiga Maiduguri sun zo daidai lokacin da dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a garin wanda dalilin haka suka kwana a cikin mota,Boko Haram ta yi amfani da wannan dama inda ta kai musu hari inda ta kona motoci da dama.

Shugaba Buhari ya kai ziyarar jaje jihar a jiya, Laraba inda har aka samu wasu mazauna garin suka mai ihun bama so.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *