fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Majalisar dokoki za ta kara wa fursunoni kudin abinci a Najeriya

Kwamitin majalisar dattawan Najeriya kan harkokin cikin gida ya soma wani yunkuri na kara wa fursunonin da ke gidajen gyaran hali kudin abinci.

Batun ya taso ne ranar Laraba lokacin da shugaban gidajen yarin kasar Mr Haliru Nababa ya je gaban ‘yan kwamitin domin kare kasafin kudin hukumar kula da gidajen yari na sekarar 2022.

A cewar kwamitin, akwai fursunoni 66,340 a gidajen gayran hali da ke fadin kasar, kuma a cikinsu har yanzu ba a yanke hukunci kan fursuna 47,559 ba.

Daga nan ne Sanata Utazi,ya gabatar da shawara a madadin kwamitin cewa ya kamata a rika bai wa kowanne fursuna N750 domin sayen abinci.

A nasa martanin, shugaban hukumar kula da giajen yarin ya ce an kara kudin kashewar fursunonin daga N450 zuwa N750 a kowacce rana a cikin kasafin kudin 2022.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *