fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Majalisar dokokin Borno ta musanta shirin tsige Gwamna Zulum

Majalisar dokokin Borno ta musanta shirin tsige gwamna Babagana Zulum.

 

Majalisar dai, ta jefa kuri’ar amincewa ga gwamnan.

 

Ku tuna cewa rahotanni sun fito a yanar gizo cewa majalisar na kokarin tsige gwamnan bisa mummunan aiki.

 

Kakakin majalisar, Abdulkarim Lawan, ya fada wa manema labarai bayan wani zaman gaggawa da suka yi ranar Juma’a a Maiduguri cewa labarin ba gaskiya ba ne.

 

A baya, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka dawo da samun wutar Lantarki a Maiduguri bayan kwashe tsawon lokaci babuta

 

Lawan ya ce majalisar ta yanke shawarar jefa kuri’ar amincewa da gwamnan ne saboda kwazon sa, musamman wajen aiwatar da ayyuka a fadin jihar.

 

Ya ce ‘yan majalisar sun yi mamakin labarin, suna masu bayyana shi a matsayin karya.

 

“Majalisar ta kada kuri’ar amincewa da Gwamna Babagana Zulum.

 

“A ka’ida, majalisar ba za ta mayar da martani ga mummunan rahoton ba, amma mun ji ya kamata mu yi magana don kar a yaudari jama’a su yarda da labarin.

 

“Wannan yana yin la’akari ne musamman da yanayin tabarbarewar tsaro a jiharmu da ma dimbin nasarorin da gwamnatin Zulum ta samu a dukkan bangarorin tattalin arziki.

 

“Gaskiyar ita ce, muna da kyakkyawar ma’amala da aiki tare tsakanin dukkanin bangarorin gwamnati a jihar,” inji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *