fbpx
Monday, November 29
Shadow

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Ganduje na karbo rancen biliyan 18.7 daga Babban bankin Najeriya

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na neman rancen N18.7bn daga babban bankin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a wata wasika da kakakin majalisar Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta a gaban ‘yan majalisar.

Ya ce amincewar ta biyo bayan bukatar gwamnan ne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin jihar.

A cewar gwamnan, rancen ya yi daidai da amincewar babban bankin Najeriya na bayar da lamuni ga daukacin gwamnatocin Jihohin kasar domin dakile illar annobar COVID-19 a jihohin.

Gwamnan ya ce N10bn daga cikin kudin za a yi amfani da shi wajen samar da karin kasafin kudin shekarar 2021.

Don haka majalisar ta amince da bukatar gwamnan na ci gaban jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dokokin jihar Jigawa ta kuma amince da bukatar gwamna Muhammad Badaru Abubakar na samun wannan adadin daga babban bankin Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *