fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Majalisar Nasarawa ta dakatar da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye kan zargin zambar daukar mutane aiki

An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Nasarawa, Hon. Luka Iliya Zhekaba (PDP- Obi 2) bisa zarginsa da hannu a aikin daukar malaman sakandare 38 a jihar na bogi.

Kakakin majalisar, Rt. Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi, bayan majalisar ta tattauna akan rahoton kwamitin Ilimi na majalisar, kan daukar malamai 366 da malaman bogi 38 a cikin albashin ma’aikatan jihar yayin zaman majalisar a Lafia.

Abdullahi ya lura cewa majalisar ba ta adawa da daukar malaman aiki, amma dole ne a bi tsarin da ya dace don yin adalci ga jama’a wajen daukar aikin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *