fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Majalisar Tarayya ta baiwa Hukumar Kwastam Umarnin mayarwa da ‘yan kasuwar Ibadan buhunan shinkafarsu da ta kwace

Kwamitin majalisar tarayya dake kula da bin doka ya baiwa hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam Umarnin mayarwa da ‘yan kasuwar Ibadan buhunan shinkafarsu data kwace.

 

Wannan Umarni ya zo ne inda majaliaar tace ta baiwa hukumar kwanaki 15 ta mayarwa da ‘ya  kasuwar da kayansu.

 

Hakan na zuwane yayin dan majalisar dake wakilar Oyo ta Kudu, Kola Balogun ya gabatarwa da majalisar koken ‘yan kasuwar ta Ojo Oba.

 

Majalisar tace wannan abinda hukumar Kwastam din ta yi ba abin amincewa bane inda tace, a bude shagunan da aka kulle sannan a mayarwa da ‘yan kasuwar kayan abinci da kudadensu da aka kwace.

 

Majalisar ta bakin kakakinta, Sanata Ahmad Lawal tace abinda Kwastam din ta yi ya sabawa dokar da Tsohon Shugaban kasa,  Olusegun Obasanjo yayi ta cewa kayan da aka shigo dasu ta barauniyar hanya, za’a iya kwace sune kawai da nisan Kilometres 40 daga kan iyakar kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

1 Comment

  • Auwal sani

    Ahmad lawal kaji tsoron Allah mu a jiharmu ta katsina kwastom suna anshe kayan mutane da tsawon kilomita 120 Sai Dan an taba Yan lelenku Zaki fitokuyi magana insha Allah bbu indazakuje…Kuma duk Nisan gona kasani akwai kunyar karshe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *