fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Majalisar zartarwa, FEC ta amince da Naira biliyan 309 don kwangilar gina hanyoyi a Legas, Kaduna, Borno da Ogun

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da gina hanyoyi biyar a kasar nan da kudin su ya kai Naira biliyan 309.

Hanyoyin sun kasance a jihohin Borno, Kaduna, Lagos da Ogun. Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar a Abuja ranar Laraba.

Ya ce titunan, gaba daya sun kai kilomita 274.9, za a gina su ne ta hanyar rukunin kamfanonin Dangote a karkashin manufofin karbar bashin haraji na gwamnatin Najeriya.

“Hanyoyin musamman sune Bama zuwa Banki a jihar Borno, kilomita 49.153; Dikwa zuwa Gamboru Ngala (Borno), kilomita 49.577; Titin Nnamdi Azikiwe wanda aka fi sani da Western Bye-Pass a jihar Kaduna, kilomita 21.477.

Hanyar samun shiga tashar jirgin ruwa mai zurfin, Sashi na I da na III a cikin jihar Legas ta hanyar Epe zuwa Shagamu Express Way, kilomita 54.24, wanda ya hada jihohin Legas da Ogun, da kuma hanyar Obele Ilaro-Shagamu, kilomita 100 a Ogun, ” in ji shi.

A cewarsa, majalisar ta kuma amince da yarjejeniyar, don saukaka aikin gina hanya mai tsawon kilomita 274 kuma “wannan zai zama  mafi girma titi na kankare da gwamnatin Najeriya ta taba bayarwa a cikin lokaci daya.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *