fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Makiyaya Basu Da Wani zabi face Daukar Bindigar AK-47>>Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce an tilasta wa Fulani makiyaya su dauki bindigogi don kare kai.

Da yake jawabi yayin bikin makon ‘yan jaridu wanda kungiyar yan jarida ta jihar Bauchi ta shirya, gwamnan ya ce makamai suna hana barayin shanu kashe su tare da kwashe shanun su.
Mohammed ya ce gazawar gwamnati na kare makiyayan ya sa suka koma neman na kare kansu.
Ya ce: “Saboda Bafulatanin yana bin al’adar makiyaya, sai ya shiga cikin daji, barayin shanu wadanda ke dauke da bindigogi, suka kashe shi kuma su tafi da dukiyarshi, wato shanu.
“Ba shi da wani zabi da ya wuce daukar AK47 saboda al’umma da gwamnati ba sa ba shi kariya, menene laifin sa; laifin gwamnati da mutane ne.
“Ba kowa bane mai laifi, saboda, a kowace kabila, akwai masu aikata laifi.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *