fbpx
Friday, April 23
Shadow

Makudan kudaden da Gwamnatocin Najeriya ke kashewa kansu maimakon yiwa jama’a aiki ne ke kawo Talauci>>Gwamna Lalong

Gwamnan jihar Filato kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, Simon Lalong ya bayyana cewa, makudan kudaden gudanar da gwamnati da gwamnatin tarayya dana Jihohi ke kashewa ne ke kara Talauci a Najeriya,  musamman a Arewa.

 

Ya bayyana hakane a ranar Asabar a Arewa House dake Kaduna inda aka yi taron tunawa da marigayi, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

 

Gwamna Lalonga yace, kamata yayi Gwamnatoci su rage yawan kudaden da suke kashewa a mayar dasu wajan raya jama’a.

 

A baya hutudole.com ya kawo muku yanda Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, har yanzu tattalin arzikin Najeriya na cikin matsala. 

Ya koka da cewa akwai matsalar rashawa da cin hanci da yawan hadimai da shuwagabannin ke dauka da kuma Albashi da ke taka rawa wajan kashe kudade da yawa a gwamnati.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *