fbpx
Monday, November 29
Shadow

Malaman Addinin Musulunci Guda 100 Ne Suka Fara Azumin Kwanaki Uku Da Addu’o’i Don Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya

Kimanin Malaman Addinin Musulunci sama da 100 ne a yau Litinin suka fara azumin kwana uku tare da addu’o’in neman zaman lafiya da hadin kan kasar Nigeria kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.

Shugaban kungiyar masu bayar da agaji na addu’o’in malam Salihu Abdullahi-Mai, yayin wani taron manema labarai a Tudun Wada, Kaduna, yace: kungiyar ta tattara malamai guda 100 da zasuyi kwanaki ukku suna gudanar da addu’o’i da azumi.
Yace “addu’o’i da azumi sun zama wajibi a garemu. Mun gayyaci masu wa’azi daga dukkan kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna da su dage da addu’o’i da azumin kan nemawa kasar zaman lafiya.
A cewarsa an ba wa masu wa’azin izinin fara addu’o’i da azumi don neman rahamar Allah kan halin tsaro a kasar nan.
“Mun yi imani cewa a kowane irin yanayi da muka samu kanmu, addu’o’i da azumi sune mafita ga dukkan matsalolin mutane saboda Allah yana sauraron bayinsa a kowane lokaci,” in ji shi.
Mista Abdullahi-Mai ya kara da cewa addu’o’i da azumin wanda aka fara a ranar Litinin da nufin yin addu’ar Allah ya ceci Najeriya da wasu sassan Afirka sakamakon tashin hankali da ta’addanci, satar mutane, rashin aikin yi ga matasa, talauci da sauran munanan ayyuka.
Ya kara da cewa yayin bikin na kwanaki uku, za a yi karatun Alqur’ani da ambaton Alkur’ani mai girma da kuma wasu addu’o’i na musamman da za a yi a Masallatai daban-daban.
Ya yi kira ga shuwagabannin na Najeriya da su tuna da su hada da Sojojin Najeriya wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a fadin duniya a cikin addu’o’insu, sannan ya yi kira ga kungiyoyin addinai su ma yi addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar da ma bayan haka.
Limamin ya ce “abin da ke faruwa a Najeriya alama ce ta cewa mun yi wa Allah laifi ta fuskoki da yawa, don haka, dole ne mu nemi gafararsa.”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *