fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Malaman kwalejojin kimiyya da fasaha sun dakatar da yajin aiki

A ranar Laraba ne kungiyar Malaman Kwalejin Kimiayya da Fasaha suka sanar da dakatar da yajin aikin da suke yi.

Sakataren kungiyar na kasa, Abdullahi Yalwa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba mai taken, ‘Dakatar da yajin aikin kasa na kungiyar.’

Yalwa ya ce kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bisa la’akari da yadda gwamnati ta fara aiwatar da abubuwa sannu a hankali kan abubuwan da ke kunshe a cikin yarjejeniyar aiki da suka sanya wa hannu.

Ku tuna cewa ASUP, a cikin bukatu tara, da aka nema sun hada da: aiwatar da sabon tsarin albashi, farfado da ilimin kere-kere, kaddamar da hukumar kasa ta fannin fasaha da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *