fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Malami ya gina rijiyoyin burtsatse 236 a Jihar Kebbi

Wasu Kungiyoyi masu zaman kansu da ke da alaka da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, sun gina rijiyoyin burtsatse 236 a yankunan karkara a fadin kananan hukumomin 21 na Jihar Kebbi.

Kungiyoyin masu zaman kansu sun hada da Kadi Malami Foundation, Khadimiiya Initiative for Justice and Development, Aisha Abubakar Malami Center for Women Debelopment da Al-Iman Charity Foundation.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Mista Malami na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Dakta Umar Jibrilu-Gwandu, ta ce ministan ya kaddamar da daya daga cikin rijiyoyin burtsatse da aka gina don ‘Yan Gudun Hijira, IDPs, da suka yi sansani a Ambursa.

Mista Jibrilu-Gwandu ya kara da cewa Malami ya yi alkawarin samar da karin abubuwan more rayuwa ga mazauna karkara a cikin jihar ta hanyar hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki.

A nasa jawabin, Hakimin Ambursa, Isah Haruna-Rasheed ya godewa ministan da kungiyoyi masu zaman kansu kan shiga tsakani.

Ya lura cewa samar da rijiyar burtsatse zai kawo karshen matsalar karancin ruwa a sansanin yan gudun hijirar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *