fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Malamin makarantar Firamare ya yiwa dalibarsa me shekaru 14 fyade a jihar Naija

Hukumar kula da ilimin bai daya a jihar Naija ta Subeb ta hukunta wani malami a jihar Naija da yawa daliba me shekaru 14 fyade.

 

Lamarin ya farune a Karabonde dake karamar hukumar Borgu ta jihar inda ake zargin malamin me suna Alhaji Usman Galadima da yin wannan aika-aika.

 

Hukumar SUBEB din dai ta dakatar da malamin.

 

Rahotanni dai sun bayyana cewa, malamin yawa yarinyar da ma wasu yaran da ya lalata barazanar kisa idan suka fadawa wani abinda ya musu.

 

Daily post ta ruwaito cewa amma wasu daga cikin daliban sun gayawa malamarsu, Maimunat Tanko wadda ita kuma ta kai maganar gaba inds aka kama malamin wanda yanzu haka ake bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *