fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Manoma sun yi mursisi sun ki biyan bashin noman da gwamnatin tarayya ta basu

Rahotanni daga Arewa na cewa manoma da aka baiwa bashi a karkashin shirin ABP da yawansu basu biya bashin ba.

 

Gwamnatin dai ta bayar da bashinne dan habaka harkar noma a kasar da burin kasar ta rika ciyar da kanta abinci ba sai an shigo dashi daga kasar waje ba.

 

Saidai matsalar tsaro ta hana lamarin tafiya yanda ya kamata. Rahoton yace daga jihar Kaduna, kasa da kaso 50 ne na manoman da aka baiwa bashin suka biya.

 

A jihar Kano kuwa kaso 80 na manoman basu biya bashin ba. Jihar Kebbi an kafa kwamitin karbo bashin amma abu ya faskara.

 

Rahoton yace, wasu manoman na ganin bashin kamar wata ganima ce da ba zasu biya ba.

 

Guardian ta ruwaito cewa, Kungiyar Manoman shinkafa ta RIFAN yanzu ta fara kai manoman kotu dan su biya bashin da ake binsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *