fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Martanin Gwamnatin Taraya ga Bishop Kuka: Abin Takaici ne, kuma abin kunya ga dan kasa yayi kalaman batanci ga kasarsa

MARTANI DAGA FADAR SHUGABAN ƘASA KAN JAWABI DA BISHOP KUKAH YAYI A GABAN MAJALISAR AMIRKA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Abin takaici ne, kuma abin kunya ga Dan Ƙasa Najeriya yayi jawabi ɓatanci kan Kasar sa a gaban wakilan majalisar kasashen ƙetare.

Tuni mun riga mun saba da irin wadan nan ziyara irin ta Siyasar wanda Ƴan adawar Siyasa keyi na ziyarar Shugabannin kasashen Ƙetare da Ƴan majalisu a Ƙasar Amirka, da Birtaniya, da Turai. Don su yada manufar su, idan da sunyi sa’a ana jin su da wani Muhimmanci a kasashen ƙetare, daga nan da suma Ƴan Najeriya dake anan gida suma sun dauke su da wani Muhimmanci.

To amma saboda suna so ajisu a ko’ina, da fadada manufar aiyukan su a kafafen yada Labaru ana gida, kada a raba daya biyu wadan nan ziyarce ziyarce ya kunshi baƙanta fuskar Kasar mu a idon masu sauraro a kasashen ƙetare da suka zabo don aiwatar da manufar su.

Nan gaba kadan Musa a rammu tabbas zamuji wasu jerin Manufofin ciki harda faruwar nuna wariyar launin fata cikin mutan Arewa, Yadda Addini guda ya mamaye harkokin Gwamnati akan Sauran addinai, da wai yadda Gwamnati bata komi don magance Matsala tsakanin Manoma da Makiyaya, da yadda Gwamnati ta kashe kudade kan Manyan aiyuka don amfanin kowa da kowa face Ƙungiya ko addinin shi mai magana. Ba shakka, don kada su bada kunya ga masu sauraron su daga kasashen yamma, ba tare da wani Ƙanshin gaskiyar cikin manufar tasu ba, Jadawalin kullum irin gudana ne ko da yaushe na nan ga wadda yake son ya sake Dubawa.

Ƴan Najeriya tuni suna tsammanin irin wadan nan karerayi daga Ƴan Adawa to amma da takaici a duk Sa’ilin da aka ce Majami’a tana kwaikwayo da kara munana abu don neman wani bukatar karan kai, ta hanyar rike Mulkin Al’umma.

Wannan Gwamnati ce kawai cikin shekaru masu yawa ta Dau batun Rikicin Manoma da makiyaya ta shirya shiri don magance kalubalen da ake samu, wanda har haka yasa ta samu yabo daga kungiyoyin agaji na kasa da kasa, ciki harda Ƙungiyar Magance fitintinu na ƙasa da ƙasa. Don ka bayyana wa masu sauraro na kasashen waje cewa wannan Gwamnati batayi komi ba karya ne tsagoran ta.

Fadin cewa wai Aiwatar da Babban aiki muhimmi tsakanin Najeriya da Jamhoriyar Nijar asara ce kawai da son kai, yayin kuma da kuma da ake irin wannan aiki tsakanin Lagos zuwa Ƙasar Benin wanda ya sauya tattalin arzikin zuwa ga alfanun dukkan kasashen namu, hakan abun takaici ne kwarai.

Babu wani nuna son kai a wannan Gwamnati don Shugaban kasa ya kasance daga arewa kuma musulmi, yayin da Mataimakin Shugaban ya kasance Kirista daga Kudu, sa annan kuma anyi raba dai dai a mukaman Gwamnati tsakanin dukka Siyoyin biyu. Duk da tsam babu inda cikin dokar kasa yace dole a raba mukaman siyasa tsakanin Kabila ko addini. Abun mamaki bakon abune ne ga shi mai tsukar ya yadda cewa kaliba Shine abu muhimmi Gurin bada mukamai gwamnati. Kuma har yanzu abun takaici ne aji wani Shugaban Majami’a guda daya tilo ya ware Ƙungiyar daya na kirista karara ya daura su kan wannan manufar.

Cikin girmamawa saboda Muhimmancin mukamin da yake rike dashi, Shide wancen Bishop ya fadi cewa Makarantun Kiristoci ne kawai Barayin daji ko Ƴan Ta’adda ke kai farmaki wannan magana babu wani gaskiya ciki. Da takaici a faɗi, to amma gaskiyar kenan cewa Wadan da tsautsayi Garkuwa da mutane, Barayin daji, da Ta’addanci ya shafi dukkan Al’umma baki daya.

Da takaici amma gaskiya cewa Daliban Makarantar Kankara a Jihar Katsina wanda suka sace su Ɓarayin daji ne da suke addini daya kamar wadda suka sacen. Irin haka ma ka iya zamo gaskiya kan Dalibai 134 na makarantar Islamiyya wanda har yanzu ake rike dasu da aka sace a Tegina jihar Naija. Kasar ta gamu da al’amura marasa dadi na sace yara mata wanda Barayin daji suka yi a Jangebe jihar Zamfara da kuma Makarantar Gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri jihar Kebbi wanda Musulmai ne kaso suka yi rinjaye da aka sace ke hanun masu garkuwa dasu, wanda Jami’an tsaro na kasar ke aiki ka-in-da-na-in don a sakosu batare da samun rauni ba.

Kai hari kan Dalibai kiristoci abun takaici ne kuma Baza’a lamunta ba, kamar yadda sace Dalibai na Sauran Addinai, Ikirarin cewa Makarantun Kiristoci ne kawai ake kaiwa hari wannan ba gaskiya bane.

A Matsayin Kasa da Al’umma, dole mu hada kai bu fassara Munafuki a yadda yake, dole ba zamu bari Banbanci Addini ya raba kawunan mu ba. Babu wani wanda ke ribata face su Munafukai idan kawunan mu bisa kalila da addini a yayin da muke tunkararsu. Barayin daji da Masu garkuwa da mutane da Ƴan ta’adda dukkan su Makiyan mutane ne wanda ya dace a tunkare su a Ɗunkule

Kamar yadda ya bayyana Ƙarara, Littafin Linjila ya fassara batun kabilanci da wariyar launi, cikin Littafin Romawa sura ta 2 aya ta 9 zuwa 10, yace… “Za’a samu masifa da tashin hankali ga duk dan Adam daya aika Mumunar aiki: na farko gashi wanda ya aikata Sa’anan ga saura mutane; to amma za’a samu Dabbaka da Girmama da zama lafiya ga duk wanda ya aikata Mai kyau”, haka nan cikin littafin Gataliyawa sura ta 3 aya ta 28 ” Babu wani Jew ko Gatale, babu wani bawa ko Mai Ƴanci, Babu Mace ba Namiji, dukkan ku daya kuke a Gurin Yesu.” ko musulmi ko kirista, munyi imani da wannan tafarki kuma mun sallama musu a tafiyar da mulki.

Babu wani dama dake akwai ga masu aiki mara kyau da kuma fitowa filoli karara su ɓatanci ga wata Ƙungiyar Kabila guda, musamman a gaban masu sauraro na kasashen ƙetare. Wannan ba Ra’ayi akasarin Al’umma Najeriya kenan ba. Da duk wani mai kalubalan ta ta a Matsayin Kasa, wanda kusan dukka mun amince muyi rayuwa guri guda cikin kwanciyar hankali, Kowa na farin ciki duk da Banbanci dake akwai, da samar da wata Ƙungiya mai taken Kasar Najeriya sama da komi. To amma mutane irin su Kukah suna duk abinda zasu iya don kawo Sabani da Jayayya tsakanin Ƴan Nijeriya.

Fiye da duk wasu mutane, Shugabannin Siyasa kona addini wanda suke wa’azantar da Girmama gaskiya dole a gani sunayin ta zahirance. Hakkin ne rikewa a zuci Dayi a zahirance.

Idan aka koma kan tarihin Majami’ar kowa ya sani, koda yaushe takan bayyana tsayawa kan gaskiya.

Lokaci ne da Sauran subi koyarwan ta.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
18 ga watan Yuni, 2021

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *