fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Maryam Yahya ta bayyana ainahin larurar dake damunta inda tace ba sihiri aka mata ba

Tauraruwar fina-finan Kannywood Maryam Yahaya ta bayyana cewa tana fama da cutar maleriya da taifod, shi ya sa aka ji ta shiru ba ta fitowa a fina-finai.

Ta bayyana haka ne a wata hira da BBC domin yin watsi da rahotannin da ke cewa tana fama da cutar da ta danganci jifan aljanu.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya yi tafiyayya zuwa gidan su tauraruwar, ya ce ta yi matukar ramewa.

Sai dai a cewarta: “Na yi taifod da maleriya ne, ina kan yi. Amma yanzu jiki Alhamdulillahi, na samu lafiya.”

Da take amsa tambaya kan raɗe-raɗin da ke cewa an yi mata asiri ko jifa, tauraruwar ta ce “gaskiya ni ba jifa ba ne ya dame ni don ban ma san shi ba.”

Ta ce ta kwashe fiye da wata ɗaya tana fama da rashin lafiya, tana mai cewa yanzu tana samun sauki sosai, “sai dai rashin ƙwari kuma dama sai a hankali ƙwari yake zuwa.”

A nasa bangare, mahaifin tauraruwar, Alhaji Yahaya Yusuf, ya ce ‘yar tasa ta kwana biyu a kwance kuma sun kai ta asibiti.

Ya kara da cewa yanzu suna haɗa maganin asibiti da na Hausa, inda ya sa malaman addini suke yi mata addu’a.

Ya ce tabbas maleriya da taifod ne ke damun ‘yarsa yana mai yin watsi da masu yaɗa jita-jitar cewa an jefi ‘yar tasa.

Matashiyar tauraruwar mai shekara 20 ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko mai suna Mansoor.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *