fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Mason Mount ya zamo dan wasa na biyu mafi karancin shekaru bayan Arjen Robben daya ciwa Chelsea kwallaye 10 a Premier League, yayin da Chelsea ta lallasa Sheffield United daci 2-1

Chelsea tayi nasarar fara jagorancin wasan ta hannun Mason Mount kafin Rudiger yayi kuskuren cin gida inda ya ramawa United kwallon, amma bayan mintina hudu Jorginho ya ciwa Chelsea kwallo ta biyu da bugun daga kai sai me tsaron raga.

Mason Mount dan shekara 22 yayi nasarar zama dan wasa na biyu mafi karancin shekaru bayan daya ciwa Chelsea kwallaye 10 a gasar Premier League, bayan Arjen Robben wanda yayi hakan yana dan shekara 21.

Kwallo guda kacal aka zira a ragar Chelsea a wasanni hudu da Thomas Tuchel ya ya fara jagoranta, wanda hakan ya kasance karo na farko tun bayan Guus  Hiddick a shekara ta 2009.

Hutudole ya samo cewa, Sakamakon wasan yasa Chelsea ta koma ta biyar a teburin gasar Premier League kuma tazarar maki guda ne kacal tsakanin tada Liverpool wadda tasha kashi daci 4-1 a hannun Manchester City yau.


Mason Mount is the second-youngest player to score 10 Premier League goals for Chelsea, after only Arjen Robben as they beat Sheffield United 2-1.

Mason Mount gave Chelsea the lead before Rudiger score an own goal to level for Sheffield United in the 54th minute and later after four minute Jorginho gave Chelsea the lead again from the spot.

Chelsea have only conceded one goal in their first four Premier League games under Thomas Tuchel – their fewest through a manager’s first four league games in charge since Guus Hiddink in February/March 2009.

Aged 22 years and 28 days, Mason Mount is the second-youngest player to score 10 Premier League goals for Chelsea, after only Arjen Robben (21y 342d).

The result means Chelsea are now fifth in Premier League standings and only a  point behind Liverpool who suffer a 4-1 defeat today at the hand of Pep Guardiola squad.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *