fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Masu ababen hawa da ke tuƙi da belun kunne (Earpiece ko AirPods) zasu fuskanci hukuncin daurin watanni shida a gidan yari – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayya ta ce direbobin da ke yin kiran ko karba kiran waya yayin tuki, ko kuma sanya na’urar magana ta kunne (AirPods ko earpiece), za su iya fuskantar hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.

Jami’in ilmantar da jama’a na hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Punch.

Kazeem ya ce tukin mota na bukatar maida hankali gaba daya kuma masu amfani da titin kada su yi wasa da rayukansu. Ya ce sabawa doka yin kira ko karba kira yayin tuki, bisa ga Dokar Kula da Hanya ta Kasa, 2012.

Yace dole ne masu ababen hawa su kauce wa yin duk wani abu da zai iya dauke masu hankali a lokacin da suke tuki domin kaucewa aukuwar hadari wanda kan iya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *