fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Masu garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield da ke Kaduna sun nemi fansar N800m

Wadanda suka sace daliban jami’ar Greenfield, wata jami’a mai zaman kanta da ke jihar Kaduna, sun tuntubi iyayensu don neman kudin fansar da suka kai na Naira miliyan 800.

Rahotannin sun nuna cewa masu garkuwan sun yi barazanar kashe daliban idan ba a biya kudin fansar ba.

A cewar rahoton, yar uwuwa daya daga cikin daliban da aka sace, Georgina Stephen, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an sace dalibai 23, wadanda suka hada da mata 14 da ma’aikatan jami’ar.

A cewar ta, masu garkuwan sun yi ta dukan daliban da suka sace, suna mai cewa idan ba a biya kudin fansar ba za su kashe su duka.

Wani mahaifin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce masu garkuwar sun kira ne don neman fansar baki daya na Naira miliyan 800.

Amma bai iya tabbatar da yawan daliban da aka sace ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *