Wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wani Fasto mazaunin Legas, Frederick Ojo Aramuwa bayan sun karbi N2m amatsayin kudin fansa.
An gano gawar Fasto Aramuwa a kusa da yankin da aka sace shi.
Majiyoyi sun ce an sace shi tare da direbansa kwanakin baya yayin da yake komawa gida Ifira, karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas.
Bayanai sun ce da farko masu garkuwan sun nemi a ba su N10m amma daga baya suka rage zuwa N2m.
Bayan biyan kudin, sai kungiyar bincike suka gano gawarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, wanda ya tabbatar da kisan Fasto Ayamure, ya ce an fara bincike.