fbpx
Monday, September 27
Shadow

Masu garkuwa da mutane sun nemi miliyan N100 don sakin basaraken jihar Kaduna da suka sace

Kusan awanni 24 da sace babban basaraken mutanen Ham, Kopp Ham Danladi Gyet Maude na karamar hukumar Jaba da ke jihar Kaduna, masu garkuwan sun sanya kudin fansa na Naira miliyan 100 kafin a sake shi.

Ka tuna cewa an sace basaraken mai shekaru 83 a ranar Litinin daga gonarsa da ke kan babbar hanyar Kwoi-Keffi.

Basaraken da aka sace yana cikin rakiyar hadimansa na tsaro lokacin da masu garkuwan suka kutsa cikin gonar da misalin karfe 2 na dare suka tafi da shi.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida cewa masu garkuwan sun je ga iyalan ne a waya da safiyar Talata kuma suka gabatar da bukatar tasu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, ASP Mohammed Jalige ya ba da tabbacin cewa rundunar‘ yan sanda ta Kaduna tana tuntuba da rundunar ‘yan sanda ta Nasarawa kan yadda za a kubutar da basaraken da aka sace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *