fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Masu garkuwa da mutane sun sako dangin Sarkin Kajuru bakwai bayan shafe watanni biyu a gurin su

Iyalan sarkin Kajuru bakwai, Alhaji Alhassan Adamu sun sake samun ‘yanci.

Sun sake samun ‘yanci a daren Laraba bayan sun shafe watanni biyu a gurin masu garkuwa da mutane

Ku tuna cewa an yi garkuwa da sarkin, tare da danginsa guda bakwai daga fadarsa a ranar 11 ga Yuli, 2021.

Bayan korafe -korafen jama’a da yin Allah wadai, an saki Sarkin bayan sa’o’i 24 bayan sace shi.

Wadanda aka yi garkuwa da su mata uku ne, maza uku da jariri.

Wani mai rike da sarauta a masarautar, Dan Iyan Kajuru Saidu Musa ya tabbatar da sakin mutanen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *